Thursday, February 8, 2007

Uwani Zakirai Da Wakar Azizu D'an Makaranta

Na fara da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jink'ai,


Sau da yawa mutane su na tunanin cewa wakar nan da Uwani Zakirai ta yi, inda ta ke juyayi kan tafiyar masoyin ta "d'an makaranta," wai Habibu D'an Makaranta ta ke cewa. Na ga irin tunanin a wani posting da Muhammad Fatuhu Mustapher ya yi a Majalisar Marubuta a yau.

Na ba Fatuhu amsa. na ce masa yawancin baitukan da ya kawo, ba haka Uwani ta ke cewa ba!
Misali ya ce ta ce:


"Motsa kalangunka
Habibu motsa kalangunka"
Ai cewa ta yi:

"Tausa kalangun ka
Nababa tausa kalangun ka..."

Haka kuma babban kuskuren da Fatuhu ya yi shi ne da ya rubuta HABIBU D'an Makaranta. To, na yafe masa wannan domin kuwa kusan kowa haka ya ke zaton zabiyar ta fad'a. Amma a zahiri, AZIZU ta ke cewa, ba HABIBU ba. Akwai wata hira da aka taba yi da marigayiya Hajiya Uwani a Rediyon Nijeriya na Kaduna inda ta tabbatar da hakan. Ina da kaset din.

Ga wani k'arin bayani kan wannan wak'a ta Azizu D'an Makaranta. A al'adar Bahaushe, ba a san shi da yi wa rubutacciyar waka kid'a ba; wannan sai Turawa! To a farkon shekarun 1970 sai wani hazikin ma'aikacin rediyo a Kaduna, wato Alhaji Yusufu Ladan (D'an Iyan Zazzau na yanzu) ya yi tunanin shin yaya wakar Hausa za ta kasance idan aka rubuta ta aka yi mata kid'a? (wato lyrics). Shi ne fa sai ya zauna ya rubuta wannan wakar ta Azizu D'an Makaranta, ya gayyato Uwani Zakirai, wadda zabiya ce a Kaduna, kuma ya gayyato Alhaji Nababa Makadi, shi ma a nan Kaduna, ya wuni tare da su su na atisayen wakar; Nababa ya na kida, Uwani ta na waka, shi kuma Yusufu Ladan ya na rike da takardar sa, ya na cin su gyara, har su ka iya wakar. Daga nan ya saka su a situdiyo a nan gidan Rediyon Nijeriya na Kaduna, aka dauki wakar kamar yadda ake jin ta a yau.

Kun ga kenan wannan wani muhimmin aiki ne da shi Alh. Yusufu Ladan ya yi, wanda har yau ba a ma damu da shi ba.

Ina so mai karatu ya sani cewa akwai wata wakar mai suna "Cha-cha-cha" wadda Danmaraya Jos ya yi tare da 'yan amshi (ina jin ai ka san ta!). Ita kadai ce wakar Danmaraya mai amshi. To ita ma rubuta ta aka yi, a wani yunkuri na kamfanin EMI, Jos, na sauya fasalin wakar Bahaushe. A hirar da na taba yi da Danmaraya (an buga ta a mujallar Fim) ya gaya mani cewa wannan yunkurin ya ci tura duk da yake wakar ta yi dadi, don haka EMI su ka watsar da shi.

14 comments:

ISLAMA said...

Assalamu Alaikum Warahmatullahim Wabarakatuh

babangida said...

Hakika naji dadin wannan bayani naka. ko a yanzu, awai wani bawan Allah, a Kano, mai suna Habibu, da yake tunkahon shi aka yiwa wannan waka. wannan baya ni nake a soke duk wata tantama. Allah ya saka da alheri.
Babangida Dangora

babangida said...

Hakika naji dadin wannan bayani naka. ko a yanzu akwai wani bawan Allah, Alhaji Habibu wanda yake tunkahon shi aka yiwa wannan waka. ko da yake wan taba jin hirar da akayi da marigayiya Uwani Zakirai ba, amma na taba jin wanda aka tabayi da mijinta.

Unknown said...

Please,yallabai idan bazaka damuba! inaso idan kana da wakokin shata da yawa ka turomun ta sarkin jama'are mana in har ban takura maka ba. Na gode

Unknown said...
This comment has been removed by the author.
Tanimu Umar said...

Allah Ya 'kara basira Ibrahim Sheme

Anonymous said...

Hakika wannan bayani ya gamsar dani kwarai.Abu daya nake nema shine rubutacciyar wakar ta Uwani Zakirai

Unknown said...

Assalamu Alaikum
Naji dadin jawabin nan, amma na dade ina neman cikakken wakar amma na gagara samu. Don Allah ko akwai yadda zan same ta wajen ka. Nagode

Imam jamil said...

wakar AZIZU DAN MAKARANT DanAllah atemaka.

Imam jamil said...

ga number whatsAp dinan Dan Allah Wanda yakeda wakar uwani zakirai ta ABDUL AZIZU DAN MAKARANT yayiwa Girman Allah yaturomin da its 07039720598 atemaka Dan Allah.

Bashir Zakirai said...

Sunana BASHIR ADO ZAKIRAI, Ni haifaffen garin zakirai ne karamar GABASAWA jihar KANO, hakika naji dadin wannan bayani na kakarmu da akayi wato UWANI ZAKIRAI. Allah ya saka da alkhairi

Abbas Musa Jega said...

Ma sha Allah

Unknown said...

Gaskiya tun ina yaro na dauka wakar marigayi professor habibu sani babura aka yiwa, sai da wani abokina ya nusantar dani na karanta wannan bayani naka sannan na gane ashe azizu take cewa. Madallah Allah ya saka maka da alheri mai yawa.

Kabir Elyakub Zakirai said...

To Nima hakika na sha yin musu da abokai na Manazarta akan wannan wakar amma yanzu na gamsu. Sai dai tambaya ta itace shin ita UWANI ZAKIRAI ta karamar hukumar Gabasawa ko kuwa akwai wata zakirai da bamu sani ba? Kabir Elyakub Zakirai